Samenvatting van de aflevering
A cikin shirinmu na yau tare da Michael Kuduson za mu yi waiwaye akan babban gangamin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya wanda shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar a Kaduna,, inda shugabannin jam’iyyar suka yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da goyon bayan Arewa. Za mu kuma ji martanin jam’iyyar ADC kan wannan ikirari, musamman batun cewa sama da mutum miliyan ɗaya ne suka halarci gangamin. Latsa alamar sauti don sauraron karin bayani.....
A cikin shirinmu na yau tare da Michael Kuduson za mu yi waiwaye akan babban gangamin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya wanda shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar a Kaduna,, inda shugabannin jam’iyyar suka yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da goyon bayan Arewa. Za mu kuma ji martanin jam’iyyar ADC kan wannan ikirari, musamman batun cewa sama da mutum miliyan ɗaya ne suka halarci gangamin. Latsa alamar sauti don sauraron karin bayani.....
Afleveringen
ADC ta magantu kan ikirarin da APC ta yi cewa Tinubu ya nada goyan bayan Arewa
BeluisterdA cikin shirinmu na yau tare da Michael Kuduson za mu yi waiwaye akan babban gangamin fara yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya wanda shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar a Kaduna,, inda shugabannin jam’iyyar suka yi ikirarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana da goyon bayan Arewa. Za mu kuma ji martanin jam’iyyar ADC kan wannan ikirari, musamman batun cewa sama da mutum miliyan ɗaya ne suka halarci gangamin. Latsa alamar sauti don sauraron karin bayani.....
Ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zargin INEC da saɓawa dokar zaɓe
BeluisterdShirin Dandalin Siyasa na wannan mako tare da Michael Kuduson ya yi duba kan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan zargin cewa Hukumar Zaɓen Najeriye, ta gaza wallafa rajistar masu zaɓe a intanet cikin wa’adin da dokar Zaɓe ta tanada. Sai dai hukumar ta ce ba ta karya doka ba. Latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
Jami'iyyar APC ta kaddamar da majalisar yaƙin neman ta a hukumance
BeluisterdShirin dandalin Siyasa na wannan mako tare da Michael Kuduson ya mayar da hankali kan ƙaddamar da majalisar yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC, da kuma martani akan zaɓen zaɓi jihar Kaduna a matsayin wurin fara gangamin Shiga alamar sauti don sauraron cikakken shirin.....
Shirin ragin kuɗin man fetur na wata 1 ya janyo cece-kuce a Najeriya
BeluisterdShirin ‘Dandalin Siyasa’ tare da Michael Kuduson a wannan mako ya yi duba ne kan matakin gwamnatin Najeriya kan shirin samar da rangwamen farashin man fetur na tsawon kwanaki 30, da martanin ’yan adawa. Sannan za mu waiwayi hukuncin Kotun Ƙoli da kuma matsayin Hukumar Zaɓen Najeriya, INEC, kan jam’iyyun siyasar da suka saɓa ƙa’idojin miƙa rajistar mambobinsu, da dai sauran batutuwan da muka tanadar muku a shirin. A daidai lokacin da ƴan Najeriya ke cigaba da kokawa kan tsadar rayuwa, musamman farashin man fetur da sufuri, gwamnatin ƙasar ta sanar da wani mataki na rage nauyin da ke kan al’umma. Gwamnatin ta ce za a sayar da man fetur bisa rangwame a gidajen mai na kamfanin man fetur na ƙasa, NNPC, na tsawon kwanaki 30, tare da bai wa masu jigilar fasinjoji fifiko. Sai dai mataki bai burge ƴan adawa ba, domin kuwa sun mayar da martani, inda suke ke tambaya ko rangwamen na ɗan lokaci zai iya magance matsalolin da suka shafi tsadar rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakke shirin.
Jawabin Tinubu na cika shekaru 66 da samun ƴancin kan Najeriya ya bar baya da ƙura
BeluisterdShirin ‘Dandalin Siyasa’ na wannan mako, ya maida hankali ne kan cikar Najeriya shekaru 66 da samun ƴancin kai, kuma yayin da ake bikin wannan rana, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ’yan ƙasar jawabi inda ya jaddada nasarorin da ya ce gwamnatinsa ta ce ta samu a fannin tattalin arziki, tare da bayyana fatansa na ganin ƙasar ta samu ƙarin wadata. Sai dai shugaban bai yi magana kan matsalar tsaro da ke ci gaba da ta zame wa wasu sassan ƙasar ƙarfen ƙafa ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Michael Kuduson.............